*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
'YAR MAFIYA
_Gajeren labari_
*Part 1-5*
© *KING BOY ISAH*
*Bissmillahir rahmanur rahim*
Godiya ga Allah madaukakin sarki da ya bani lafiya kwanciyar hankali.
*Tsira da amincin Allah*
Su kara tabbata ga shugaban mu annabi Muhammad S.A.W
*NA SADAUKAR DA WANNAN GAJERAN LABARIN GA YAN GROUP DIN. (KING BOY ISAH NOVELS) INA MATUKAR JI DAKU INA ALFAHARI DAKU*
*KARSHEN PAGEN BAYA*
~......................~
_*L*abarin ya fara ranar wata laraba da yamma. Ranar ina cike da bacin rai sosai ba. Duk duniya tayi min kunci. Sosai nake nadamar auren tallaka a rayuwa ta. Saboda tsabar talaucin mijina a gidan in nayi tuwo yau shi zamuci da da dare. Da rana kuma garin kwaki. Da dare ma tuwan jiya zamuci haka da safe. Kasancewar mu biyu ne kadai a gidan, Shekarar mu 4 Allah bai bamu haihuwa b Sau tari ina kai kara gidan mu, Daga naje sai su fara min wata nasiha dake shiga ta kunnen dama tana fita ta kunnen hagu. Ya kasance duk sanda nakai karar a kan talaucin mijina sai Mamar mu tace, "Me yasa baki da hakuri Safiyya. Shin baku san arziki na wajen Allah bane? Haba Safiyya me yasa kike abu kamar marar ilimi? A rayuwa in kana duba na sama da kai bafa zaka taba gode wa Allah ba. Amma a duk sanda kayi duba i zuwa na kasa da kai, Zaka gode wa Allah. Allah nasan masu godiya a gare shi. Kuma yana kara musu. A duk lokacin da sukayi godiya a gare shi". Duk sa'ilin da Mamar mu ta fadi haka ni kuwa sai ince "Mama har a kwai matalauta na kasa da mu? Karfa ki manta kwana biyu muke bamu dora tukunya ba. Kullum cikin zarya nake daga gidana zuwa shagon sai da garin kwaki". In mum taji haka sai tayi murmushi tace, "Safiyya kenan. Safiya a duniya akwai wanda basa samun abincin Safe, Rana, Dare. Wasu suna cin na Safe da dare ne kawai su tsallake rana. Wasu kuma sukan ci da Safe da rana shikenan suyi hakuri kuma sai gobe. Sannan kuma duk wannaj cin abincin da nake gaya miki ba lalai ne suna ci suna koshi ba. Safiyya akwai garin da ake samun gidan da Ba a dora girki sai sati-sati._
_Sai dai su sha fura safe rana dare. Safiyya ki gode wa Allah da ya bawa mijin ki halin saya miki garin ma. Kuma ki roki Allah da ya karawa mijin ki arziki. Domin talauci da aziki ba mutumin da ke zuwq da su duniya. Kowa a duniya yake sama kuma ba wayo ke bada su ba. Ko mako, ko Dabara. Aa Allah shi yake bayarwa ga duk wanda yaga dama". Duk da nasan maganganun Mama gaskiya ne amma bani daukar ko daya a ciki. Dan ni babban gurina shine in auri hamshakin mai kudi in ringa watayawa da walwalata. Amma ba talaka ba irin mai gidana. Ni dai in zanci mai kyau in sa mai kyau. In rike faskekiyar waya. A samo min yan aiki da driver to fa ni ban damu da taya aka samu kudin nan ba. Ni kam har kisa ina iyayi saboda kudi. Bansan wacce kaddarar ce ta hada ni aure da Malam bala ba. Kamar kullum haka yauma ya miko min naira Arba'in da zai fita wai kudin abincin rana ne. Ban ko kalle shi ba. Ya dade yana miko min amma naki karba. Da ya gaji sai ya wullar da su a nan ya kama hanya ya wuce kasuwa wajen dakon shi. Daki na shiga na kwanta ina tunanin rayuwata. Ina ta sake-sake ina wassafa yanda rayuwata zata kasance da ace ina cikin dola. Ana cikin haka barci ya kwashe ni ban tashi ba sai bayan la'asar. Ai kuwa na tashi da masifaffiyar yunwa. Har wani jiri nake ji yana debata domin rabona da abinci tun tuwan safe. Ina fitowa daga daki mukayi ido hudu da 40 din da mijina ya wullo min. Tsaki naja a zuciya nace "Yo me 40 naira zata wa mutum. Ni kam gaskiya na gaji da gari da sugar". Hayaniya naji a makwabtan mu. Hakan yasa na tuno da cewar ashe fa Maryam ta haihu yau da safe. Makwabciya ta. Ai kuwa na dauki gyale na yafa na fito zuwa gidan a tunanina baza a rasa abinci ba ko kunu. Bayan na shiga mun gagaisa da mutane. Na shiga baza ido ko zan ga abinci. Abun haushi ko loma daya banga wulginta ba. Sai faman hira suke ba abunda yasha musu kai. Ji nayi yunwa na neman sabautani da sauri na baro gidan na zo na tsince 40 din na fito na jawo gidan da nufin zan je shago in sayo Gari da suga. Tafe nake cike da bacin rai duk duniya tayi min kunci. Saboda bakin talaucin da ya min kanta. Cik! Na tsaya ina duban kasa. Ina kara kurawa wajen ido. Murje idanuna nayi domin tantamar nake anya kuwa abunda suke nuna min gaske ne. Tabbas gaskiya ne naira duba ce sabuwa fal! A kasa. Wani farinciki da jin dadi ne suka ziyarci zuciyata lokaci guda. Ji nayi kamar an bani kyautar million. Nan da nan na fara sake-saken abunda zanyi da ita. Lokacin da na waiga hagun da dama naga ba mai kallona na duka na kai hannu da niyar in dauki dubun.Da kai hannuna na bace Bat! Sai tsintar kaina nayi a wani daki._
_Sama da kasa na kalle dakin ni kam a duk tsawan rayuwata ko dakunan kawayen na matan masu hannu da shuni da nake ziyarta ban taba shiga daki mai kyau irin wannan ba. Glof din dakin kadai bana kananun kudi bane. Sai kyalli yake. Tsoro ne ya lulube ni nan take na fara karkarwa. Gefena na kalla wasu mutanen ne mace biyu namiji daya. Dukkan su ba ramamme. Dan dayar macen ma naga kibarta har tayi ovar. Hannun na dora a kai, cikin kukan da ba hawaye nace, "Wayyo Allah na na shiga uku ni Safiyya. Dan Allah ina ne nan kuka kawo ni. Dan Allah ku mayar dani gida". Dariya namijin ya gagabe da ita, Daya daga cikin matan ta kalle ni tace, "Baiwar Allah nan gida ne da kullum sai yayi baki amma duk bakon da ya shigo baya fita. Nan gida ne wanda ran dan adam ba a bakin komai yake ba. Nan gidan ne da suka dauki kashe mutum kamar kashe sauro ko cinnaka. Yar uwa nan gida ne da bana tunanin zaki taba kubucewa daga cikin sa. Bari in fayyace miki nan dai GIDAN YAN MAFIYA NE". Ra! Ras! Gabana ya fadi jikina ya dauki kyarma. Dan tsabar tsoro. Matar taci gaba da cewa. Kin ganmu nan da mu biyar ne, jiya da shekaran jiya aka yanka sauran. kiwan mu ake kamar dabbobi. Dukan mu lokacin da muka shigo gurin nan bamu kai haka kiba ba. Naman mutane shine abincin mu shi yake hura mu muke hawa haka ba wuya". A tsorace nace "Naman mutun?, to Wallahi ni bazanci ba". Murmushi tayi tace.... .. ................................._
Autan writers KingBoy:

Comments
Post a Comment